Description
A wani sabon salo na adawar siyasa dake ruruwa a jihar Kaduna, musamman a tsakanin tsagin gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da na Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, an samu furucin kalaman tunzura da batanci. NAIJ.com ta ruwaito a wani dan majalisar dokokin jihar Kaduna dake wakiltar al’ummar karamar hukumar Igabi ta yamma, kuma guda cikin na hannun daman gwamnan jihar Kaduna, Honorabul Yusuf Zailani ya sanya kyautar miliyoyin kudi ga duk wanda ya kawo masa gashin Shehu Sani. KU KARANTA: Ruwa yayi tsami: Hukumar tsaron sirri ta janye jami’anta dake tsaron Saraki da Dogara Zailani, mai tsawatarwa a majalisar jihar ya bayyana wannan magana ne a yayin wani taron yan siyasa magoya bayan gwamna El-Rufai da aka shirya a gundumar Rigasa na jihar Kaduna. inda yace: “Duk wanda ya asko min gashin Sanata Shehu Sani kuma ya kawo min gashin zan bashi kyautar kudi naira miliyan 5!” Shehu Sani da Yusuf Zailani Shi dai Sanata Shehu Sani ya yi suna wajen tara gashi akansa, wanda aka fi sani da Ciko ko Afro da harshen Turanci, tun fiye da shekaru 15 da suka gabata, don haka gashin ta zama wata alama ta gane Sanatan a duk inda ya shiga. Sai dai har zuwa yanzu Sanatan bai ce uffan ba game da kwangilar farautar gashin nasa da dan majalisa Yusuf Zailani ya bayar, amma masana siyasa sun yi Allah wadai da wannan magana, inda suka ce hakan ka iya jefa rayuwar Sanatan cikin hadari. Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Read more: https://hausa.naija.ng/1173203-wani-dan-majalisa-ya-sanya-tukuicin-n5000000-ga-duk-wanda-ya-yanko-masa-gashin-shehu-sani.html#1173203
Additional Data
|
Date of Original Posting of the Speech: | Jun 04 2018 |
Date of Reporting: | Jun 04 2018 |
|
Has this Hate Speech Been Used Before?: | Yes |
Does the text use coded language?: | Yes |
|
|
Medium of Dissemination: | Newspaper |
|
|
|
|
|
|
What Language was the hate speech written in?: | Hausa English |
|
Does the speech item does any of the following? (Select all that apply): | Suggest that the audience faces a serious threat or violence from another group |
|
Does the hate speech call audience to action?: | Not sure |
|
|
|
|
|
|
|
|
Was the hate speech a reply to a larger post, or an independent post?: | Yes |
The Speech is Targeting?: | Political party |
People Likely to React to the Speech Are?: | Political party |
|
Gender of the Speaker: | Male |
|
|
Who is the speaker?: | An anonymous commenter |
Are they an influential speaker?: | No |
What is the Source/Basis of Speaker's Influence?: | Other |
|
Is the speaker a prominent purveyor of hate speech?: | Yes |
Based on responses, how inflammatory is the hate speech?: | moderate 2 |
Credibility: |
 |
 |
0 |
|
Leave a Comment